Matthew 4

Gwajin Yesu

1Saʼan nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada domin Iblis yǎ gwada shi. 2Bayan ya yi azumi yini arbaʼin da kuma dare arbaʼin, sai ya ji yunwa. 3Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi.”

4Yesu ya amsa, ya ce, “A rubuce yake: ‘Ba da burodi kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’
M Sh 8.3


5Saʼan nan Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya sa shi ya tsaya a kan wuri mafi tsayi duka na haikali. 6Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, dira ƙasa. Gama a rubuce yake:

“ ‘Zai umarci malaʼikunsa game da kai,
za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’
Zab 91.11, 12


7Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa: ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’
M Sh 6.16
8Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. 9Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in ka durƙusa ka yi mini sujada.”

10Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake: ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’
M Sh 6.13


11Saʼan nan Iblis ya bar shi, malaʼiku kuwa suka zo suka yi masa hidima.

Yesu Ya Fara Waʼazi

12Da Yesu ya ji labari cewa an sa Yohanna a kurkuku, sai ya koma zuwa Galili. 13Barin Nazaret, sai ya je ya zauna a Kafarnahum, wadda take a bakin tafki wajen Zebulun da Naftali—  14don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa:

15“Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali,
hanyar zuwa teku, a bakin Urdun,
Galili ta Alʼummai— 
16mutanen da suke zama cikin duhu
sun ga babban haske;
a kan waɗanda suke zama a ƙasar inuwar mutuwa kuwa
haske ta haskaka.”
Ish 9.1, 2f


17Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara waʼazi yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”

Kiran Almajirai na Farko

18Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ʼyanʼuwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗanʼuwansa Andarawus. Suna jefa taru a tafki, gama su masunta ne. 19Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masuntan mutane.” 20Nan da nan suka bar tarunsu suka bi shi.

21Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ʼyanʼuwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗanʼuwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya tarunsu. Yesu ya kira su, 22nan take suka bar jirgin ruwan da mahaifinsu suka kuwa bi Yesu.

Yesu Ya Warkar da Marasa Lafiya

23Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majamiʼunsu, yana waʼazin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane. 24Labarinsa ya bazu koʼina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su. 25Taron mutane mai yawa daga Galili, Dekafolis,
Wato, Birane Goma
Urushalima, Yahudiya da kuma yankin hayin Urdun suka bi shi.

Copyright information for HauSRK